FATHERS LOVE LETTER .COM
  • Home
  • About
    • About
    • Contact
    • Copyright
    • Donate
    • FAQ
    • Our Vision
    • Privacy Policy
    • Terms of use
    • The Story
    • What We Believe
  • Media Formats
    • Media Center
    • HD Video
    • Vertical Video
    • Video History
    • Stores
    • Text
    • Audio
    • Kids FLL
  • Languages
  • God and You
  • FLL Book
    • Devotional Index
    • Free Audiobook
    • Free eBook

Hausa
Father's Love Letter

The Hausa Father's Love Letter is currently available
in the following formats:
1. An instrumental video version
2. An A4 single page PDF
3. An 8.5 x 11" single page PDF
4. An unformatted online text version
(Please feel free to copy the Hausa text and design your own version).

Hausa Father's Love Letter Instrumental Video

Video Courtesy of Berge Boyadjian

Hausa Father's Love Letter PDF files

Picture
Hausa Father's Love Letter A4 PDF
Right click to download / Left click to view online
DOWNLOAD THE HAUSA FLL A4 PDF FILE
Picture
Hausa Father's Love Letter 8.5 x11" PDF
Right click to download / Left click to view online
DOWNLOAD THE HAUSA FLL 8.5 X 11" PDF FILE
Hausa Father's Love Letter
Wasika Mai Nuna Yawan Kauna
Daga Wurin Allah Zuwa Gare Ku.

Yaya Na,


Mai yiwuwa baku san ni ba,
amma ni na san kome game da ku.
Zabura 139:1

Da zaman ku da tashin ku duk na sani.
Zabura 139:2

Na saba da duk al'amuran ku.
Zabura 139:3

Har gashin kan ku ma duk a kidaye ya ke.
Matta 10:29-31

Na halicce ku cikin siffa ta.
Farawa 1:27

Ta gare ni ne kuke rayuwa,
kuke motsi, kuke kuma kasancewa.
Ayyukan Manzanni 17:28

Ku ma zuriya ta ce.
Ayyukan Manzanni 17:28

Na san ku tun kafin a yi cikinku.
Irimiya 1:4-5

Tun kuna ciki na maishe ku abin gado na.
Afisawa 1:11-12

Ba ta hanyar kuskure na yi ku ba,
kwanakin ku duka na rubuta a littafi na.
Zabura 139:15-16

Ni na halicce ku,
na kuma kayyade in da za ku zauna.
Ayyukan Manzani 17:26

Yadda na yi ku abun banmammaki ne.
Zabura 139:14

Ni na harhada ku a cikin mahaifan ku.
Zabura 139:13

Tun da aka haife ku, ina kiyaye ku.
Zabura 71:6

Wadanda basu san ni ba,
ba za su gane maganata ba.
Yahaya 8:41-44

Ba na nisa ko fushi,
ina da cikakiyar kauna domin ku.
1 Yahaya 4:16

Ina marmarin nuna maku ainihin kauna.
1 Yahaya 3:1

Domin ku yaya na ne, ni kuwa Uban ku ne.
1 Yahaya 3:1

Ina ba da kyawawan kyautai fiye da ubanni na duniya.
Matiyu 7:11

Ni ne Uba na kwarai.
Matiyu 5:48

Kowace kyakkyawar baiwa daga wuri na ta ke.
Yakubu 1:17

Dukkan komai nawa ne zan kuma biya duka bukatun ku.
Matiyu 6:31-33

Shirin alheri ne na ke da shi domin ku.
Irimiya 29:11

Ina kaunar ku da madawwamiyar kauna.
Irimiya 31:3

Yawan kyakyawan tunani da nake da shi domin ku,
in da za'a kidaya shi za ya fi yashin teku yawa.
Zabura 139:17-18

Ina murna da ku ta wurin raira waka.
Zafaniya 3:17

Bazan fasa nuna maku alheri ba.
Irimiya 32:40

Ku zababbiyar jama'a ta che.
Fitowa 19:5

Ina marmarin dasa ku a wanan
kasa da aminchi da zuchiya daya.
Irimiya 32:41

Ina so in nuna maku manyan
al'amura masu girma da banmamaki.
Irimiya 33:3

Idan kun neme ni da dukan ranku,
za ku same ni.
Maimaitawar Sharia 4:29

Ku nemi farin cikinku a wuri na,
zan kuwa biya maku bukatunku.
Zabura 37:4

Ni ne mai aiki a zuchiyar ku.
Filibiyawa 2:13

Ina da ikon aikatawa fiye da yadde kuke tsammani.
Afisawa 3:20

Ni ne mai ba da madawwamiyar ta'aziyya.
2 Tasalonikawa 2:16-17

Ni ne kuma Allah na dukan ta'aziyya.
2 Korantiyawa 1:3,4

Lokachin da kuna bachin zuchiya ko damuwa,
ina kusa.
Zabura 34:18

Zan rungume ku yadda makiyayi ke yi.
Ishaya 40:11

Wata rana zan share maku dukkan hawaye.
Wahayin Yahaya 21:3-4

Bakin ciki, da kuka, da azaba duk zan dauke.
Wahayin Yahaya 21:3- 4

Ni Uban ku ne kuma ina kaunar
ku yadda nake kaunar da na, Yesu.
Yahaya 17:23

Ta wurin Yesu ne kauna ta take bayyanuwa.
Yahaya 17:26

Shi ne ainihin kamanni na.
Ibraniyawa 1:3

Ya zo ya nuna yana goyan bayanku.
Baya gaba da ku.
Romawa 8:31

Ba na lisafta laifofin ku.
2 Korantiyawa 5:18-19

Yesu ya mutu domin ya sulhunta ku da ni.
2 Korantiyawa 5:18-19

Mutuwar sa ta zama cikakkiyar
bayyanuwar kaunar sa domin ku.
1 Yahaya 4:10

Na ba da komai nawa domin in kaunace ku.
Romawa 8:31-32

In kun karbi kyautar da na Yesu,
kun kuwa karbe ni.
1 Yahaya 2:23

Ba abu da zai sake raba ku da
kaunar da nake da ita domin ku.
Romawa 8:38-39

Akwai baban buki da za a yi a sama in kun zo gida.
Luka 15:7

Ni ne Uba. Ni ne Uba har'abada.
Afisawa 3:14-15

Tambayar ita ce…
za ku zama yaya na?
Yahaya 1:12-13

Ina jiran ku.
Luka 15:11-32


Da yawan kauna,
Uban ku.
Allah mai Tsarki


ACKNOWLEDGEMENTS / PERMISSION:
Special thanks to Talitha Tukura for translating the Father's Love Letter into Hausa.
Please feel free to copy and share all of the resources on this page as long as you do so free of charge.

About Us

About
The Story
Copyright

Get Involved

FAQ
Terms of Use
Our Websites

Connect

Contact
Privacy Policy
Donate
© COPYRIGHT 2022. ALL RIGHTS RESERVED.
  • Home
  • About
    • About
    • Contact
    • Copyright
    • Donate
    • FAQ
    • Our Vision
    • Privacy Policy
    • Terms of use
    • The Story
    • What We Believe
  • Media Formats
    • Media Center
    • HD Video
    • Vertical Video
    • Video History
    • Stores
    • Text
    • Audio
    • Kids FLL
  • Languages
  • God and You
  • FLL Book
    • Devotional Index
    • Free Audiobook
    • Free eBook